ECOWAS ta kafa gudauniya kan Ebola
Shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika wato Ecowas su 15, sun tashi daga wani taro a birnin Accra na kasar Ghana da yammacin ranar Alhamis da kafa wata gidauniya kan cutar Ebola.
Shugabannin sun tattauna ne kan yadda zasu tunkari cutar mai kisa ta Ebola da ta barke a wasu kasashen yankin da kuma matsalar tsaro da kawo zaman lafiya a yankin.
Kafa gidauniyar dai shi ne sakamakon tattaunawar da shugabanin suka yi kan cutar ta Ebola a wajen taron, sai dai ya zuwa yanzu shugaban Najeriya ne kawai ya bayar da gudunmuwa gare ta.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ba da gudunmuwar dala miliyan uku na Amurka ga gidauniyar yaki da cutar ta Ebola a kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo inda cutar ta kashe daruruwan mutane ya zuwa yanzu.
Comments
Post a Comment
COMMENT HERE